Rahotanni sun nuna cewa ‘yan gudun hijira daga al’ummar Yelwata da ke karamar hukumar Guma a jihar Binuwai sun nuna rashin amincewarsu da halin da suke ciki a sansanin da gwamnatin jihar ta samar.
Mutanen da suka rasa matsugunansu sun yi sansani ne a Kasuwar Duniya da ke Makurdi, biyo bayan hare-haren da wasu masu dauke da makamai suka kai wa al’umma, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da kone gidaje.
Shugaban kasa, Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Arewa ta tsakiya, sun ziyarci jihar Binuwai a ranar Laraba, domin ganawa da masu ruwa da tsaki kan yadda za a kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.
Shugaban ya kuma ziyarci asibitin da wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su ke karbar kulawa.
Masu zanga-zangar sun fita kan titunan Makurdi tare da toshe duk wasu manyan hanyoyin shiga sansanin na wucin gadi da ke kan titin George Akume a birnin Makurdi, domin nuna rashin ɓacin ransu kan cin zarafi da suke zargin an yi musu tun lokacin da suka isa sansanin.