Gwamnatin Najeriya ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani ga shawarwarin da ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya bayar na gargadin dukkan Amurkawa da su kaurace wa duk wasu ofisoshi na soji da na gwamnati a Abuja.
A martanin da ta mayar, gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa Abuja ta kasance cikin aminci ga ‘yan kasa da masu ziyara baki daya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ministan yada labarai Muhammad Idris ya fitar.