Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC da jam’iyyar PDP za su yi wani zama don magance rikici tsakaninsu kan taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga watan Yuni.
Wannan dai na zuwa ne bayan takaddamar da ta kunno kai a tsakanin bangarorin biyu kan rashin bin ka’idojin gudanar da taron, a cikin wasikar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya tura wa INEC mai dauke da sa hannun Ambasada Umar Damagum ya sanya wa hannu kawai.
A cikin wata wasika da ta aike wa Damagum, INEC ta tabbatar da cewa za ta yi taro da shugabannin jam’iyyar a yauTalata, a dakin taro na hukumar da ke Abuja.