Jam’iyyar Labour Party ta sake rasa wasu ‘yan majalisa guda biyu da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, a daidai lokacin da sauye-sauyen siyasa ke kara kamari gabanin babban zaben 2027.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a ranar Alhamis ya sanar da sauya shekar Sanata Neda Imasuen, mai wakiltar Edo ta Kudu, yayin zaman majalisar a Abuja.
A cikin wasikar da ya aike wa majalisar dattawa, Imasuen ya ce matakin nasa ya biyo bayan tattaunawa da al’ummarsa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da kuma magoya bayansa.
Shima dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa/Kudu Chimaobi Atu, ya fice daga jam’iyyar Labour zuwa APC.
Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ne ya sanar da sauya shekar sa a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Atu, ya alakanta ficewarsa da rikicin cikin gida na jam’iyyar Labour, wanda ya ce ya yi illa ga ayyukansa na majalisa.



