Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta fitar da wata sanarwa a shafinta na X inda ta gargadi mazauna jihar game da shigar banza cewa, tarar dubu 50 ce doka ta tanadar ga duk masu wannan dabi’a.
Rundunar ‘yan sandan ta fitar da gargadin ne a ranar Asabar dauke da wani rubutu mai taken “wasu dokoki da ba ku sani ba, amma duk sati za mu rika kawo muku su don ku san su”
Sanarwar kuma ta kara da cewa, tun da ba ku son sanya kayan da za su rufe tsiraicinku, gwamnati ta shirya hukunta duk wanda ya karya dokar.



