Kwamandan birget na 17 ta Rundunar Sojin Nijeriya da ke Katsina, Birgediya-Janar Babatunde Omopariola ya umurci jami’ansa da su kawo karar duk sojan da suka gani yana shaye-shaye.
Kwamandan ya ba da umurnin ne a ranar Asabar a Katsina yayin bikin ranar Sojoji ta 2025.
Babatunde ya bayyana cewa, ta’ammuli da miyagun kwayoyi rage karfi da gurgunta rayuwar jami’an ne.
Ya kuma gargadi jami’an da su guji ta’ammuli da miyagun kwayoyi musamman a cikin bariki.