Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana a kotun tarayya da ke Abuja da safiyar Litinin, 30 ga Yuni, 2025, domin fuskantar tuhumar batanci da ake yi mata kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Gidan talabijin na Channels ya ruwato cewa ta iso kotun tare da mijinta, Emmanuel Uduaghan, da ‘yar gwagwarmaya Aisha Yesufu, da kuma magoya bayanta.
A cewar karar da gwamnatin tarayya ta shigar ta bakin ofishin Antoni Janar na kasa, Natasha na zargin cewa Akpabio da Bello na shirin hallaka ta, a wani shiri da aka watsa kai tsaye a talabijin.
A zaman baya ranar 19 ga watan Yuni, kotu ta ki amincewa da bukatar kama ta, inda alkalin ya ce ba a isar mata da sammaci ba kafin zaman, inda ake sa ran mai Shari’a Mohammed Umar ne zai jagorancin zaman sauraron karar.