Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ce babu wani shiri da Buhari ya yi don kawo wa gwamnatin Bola Tinubu cikas.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Garba Shehu ya bayyana haka ne a Abuja yayin hira da manema labarai gabannin kaddamar da littafinsa “According to the President” da za a kaddamar a ranar 9 ga watan Yuli.
Sa’annan ya karyata rade-radin da ke cewa Buhari ya bar cire tallafin man fetur zuwa lokacin barin mulki don jefa Tinubu cikin matsala, yana mai cewa su duka ‘yan jam’iyyar APC ne, kuma Buhari ba zai cutar da gwamnatin da ta gaje shi ba.



