Sarki Charles III ya sanar da dakatar da amfani da jirgin masarautar Burtaniya tun zamanin Sarauniya Victoria, domin rage kashe kudi da inganta masarauta.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito mai kula da harkokin kudin fadar, James Chalmers, ya ce za a maye gurbin jirgin da jiragen sama biyu saboda tsadar kula da shi, kuma aikin janye jirgin zai fara ne a 2026.
Rahoton kudin masarautar ya nuna cewa kudin kula da ayyukan sarauta ya tsaya a Yuro miliyan 86.3 a shekarar 2025, amma zai karu zuwa Yuro miliyan 132 a badi.
Sarki Charles ya ce zai yi bankwana da jirgin cikin girmamawa, musamman taragon da aka kera masa tun shekarun 1980.