Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da bayar da tallafin karatu ga daliban kungiyar kasashen gabashin Karebiyan OECS don yin karatu a jami’o’in Najeriya, daga shekara mai zuwa.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Gros Islet a ranar Litinin tare da Firayim Ministan Saint Lucian Philip J. Pierre, Shugaba Tinubu ya ce tuni aka fara shirin kuma za a aiwatar da shi a karkashin wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasashe mambobin kungiyar OECS.
Ya kuma tabbatar da cewa suna ci gaba da tattaunawa kan bai wa jami’an diflomasiyya daga kasashen OECS izinin shiga Nijeriya ba tare da biza ba.
