Tsohon gwamnan Akwa Ibom, Victor Attah, ya yi kira da a samar da sabon kundin tsarin mulki kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauka daga mulki, yana mai gargadin cewa Najeriya za ta kara fadawa cikin matsaloli idan hakan bai faru ba.
Attah wanda jaridar Punch ta ambato na bayyana kundin tsarin mulkin 1999 a matsayin mai cike da kura-kurai da rashin dacewa da yanayin Najeriya.
Ya ce Tinubu shi ya fi dacewa da jagorantar sauyin, duba da irin kalubalen da ya fuskanta a matsayin gwamnan Legas game da tsarin mulkin yanzu.
A karshe, Attah ya bukaci a gina sabon tsarin da zai karfafa hadin kai, adalci da ci gaban kasa, yana mai cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta dauki wannan matsaya da aka dade ana son cimma wa.