Majalisar dinkin duniya ta amince da kasafin dala biliyan 5.4 don aikin wanzar da zaman lafiya ga kasashen Duniya a shekarar 2025-2026
Amincewa da kasafin ya biyo bayan da wakilai suka shafe makonni suna cimma yarjejeniya, a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki ke gargadi kan matsalolin kudade da ake fuskanta.
Duk da cewa kasafin na bana bai kai na shekarar da ta gabata ba, za a yi amfani da shi wajen aikin wanzar da zaman lafiya a kasashe 12 na Duniya.
Kasashen da za ayi aikin wanzar da zaman lafiyar sun hadar da Uganda da Italiya, sai kuma Lebanon da sauran su.
Shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na da akalla jami’ai dubu 70 a yankin gabas ta tsakiya, nahiyoyin Afirka da Turai kamar yadda rahoton jaridar Daily Nigerian ya tabbatar.