Oluwatunbosun Awe, mataimaki na musamman ga Sanata Olajide Ipinsagba mai wakiltar yankin Ondo Arewa a Majalisar Dattawa, ya yi murabus daga mukaminsa bisa albashin N20,000 da ake biyansa a kowane wata.
Awe, wanda ke matsayin jami’in hulɗa da mazabu a gundumar Isowopo Ward 2, karamar hukumar Akoko North East ta jihar Ondo, ya bayyana murabus dinsa a cikin wata wasika da aka fitar a ranar Laraba.
Ya ce albashin bai dace da halin tattalin arzikin Najeriya a yanzu ba, musamman duba da sabon albashin ƙasa na N70,000 da aka amince da shi kwanan nan.
Ya bayyana cewa duk da roƙon da ya yi wa Sanata Ipinsagba kan a duba albashinsa, ba a ɗauki wani mataki ba, kodadai makusantan sanatan sun yi watsi da dalilan murabus din nasa, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta tabbatar.



