Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar sojin kasar da sauran hukumomin tsaro da su tunkari kuma su kawar da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, ‘yan tawaye da masu neman ballewa da ke barazana ga zaman lafiya da hadin kan ƙasar.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Mataimakinsa, Kashim Shettima, a lokacin bikin Ranar Sojin Nijeriya ta 2025 (NADCEL), wanda aka gudanar a Filin Murtala da ke Kaduna.
Shugaban kasar bai ɓoye gaskiya ba wajen bayyana irin manyan barazanar da Nijeriya ke fuskanta, inda ya gargadi cewa ta’addanci, tayar da ƙayar baya, fashi da makami da ƙoƙarin ballewa daga ƙasa ba ƙaramin abu ba ne.



