Rundunar tsaron sama ta Nijar ta yi ruwan wuta ga wani gungun ‘yan ta’adda a lokacin da suke wani taron tattauna shirin yiwuwar kai wani sabon hari kan sansanin sojin kasar da misalin karfe 6 na safiyar Lahadin nan kamar yadda rundunar sojin kasar ta ruwaito a shafinta na facebook.
Kazalika rundunar ta ce a yayin wannan barin wuta ta kona babura da motoci tare da lalata wadansu kayayyakin ‘yan ta’addar da dama.
Wannan nasara dai na zuwa ne bayan wadansu tagwayen hare-hare da ‘yan ta’addar suka kai a ranar Juma’ar da ta gabata a garuruwan Bouloundjounga da Samira cikin karamar hukumar Gotey da ke jihar Tillaberi inda nan ma jami’an tsaron suka yi nasarar hallaka wadansu mahara 41 tare da kwace tarin makaman yaki da babura yayin da sojojin kasar 10 suka kwanta dama, wadansu 15 suka jikkata.