Fasinjojin jiragen sama da ke tashi daga Nijeriya na biyan ɗaya daga cikin mafi tsadar haraji da kuɗaɗen jirgi a nahiyar Afirka, inda matsakaicin kuɗin da ake biya ga kowane fasinja a tafiyar ƙetare ya kai dala $180 — kusan sau uku na matsakaicin kuɗin nahiyar wanda yake dala $68, a cewar wani sabon rahoto daga Ƙungiyar Kamfanonin Jiragen Sama na Afirka (AFRAA).
Nazarin, mai take AFRAA Taxes and Charges Study Review 2024, wanda jaridar PUNCH ta samu, ya bayyana yadda yawan haraji da kuɗaɗe ke hana bunƙasar harkar sufurin jiragen sama a Afirka tare da ɗora wa matafiya nauyin da bai kamata ba.
Nijeriya na matsayi na uku cikin ƙasashen da ke da mafi tsadar haraji da kuɗaɗen tikitin jirgi a Afirka, tana bin bayan Gabon da Saliyo. Sauran ƙasashen Yammacin Afirka da suka shiga cikin jerin goma na ƙasashen da suka fi tsadar haraji a zirga-zirgar jiragen sama sun haɗa da Nijar, Benin, da Ghana.



