Rundunar sojin sama ta Najeriya, karkashin Operation Hadin Kai, ta kai gagarumin farmaki na sama kan sansanonin ‘yan
ta’adda a Dutsen Mandara da ke jihar Borno a ranar Lahadi.
Dutsen Mandara na kan iyakar Najeriya da Kamaru, kuma an tabbatar da cewa ya zama mafakar mayakan Boko Haram na bangaren Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS).
A wata sanarwa da mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar a Abuja, wadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ya ce an kai hare-haren ne bayan bayanan leken asiri sun tabbatar da tarin kayan aiki da zuwan manyan kwamandojin JAS a yankunan Wa Jahode da Loghpere.