Stephen Elwangu, matashin dan siyasa a kasar Uganda, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2026, domin kalubalantar Shugaba Yoweri Museveni wanda ya kusan ninka shekarunsa gida uku.
Elwangu ya kaddamar da wata kungiya da ya kafa mai suna People’s Leadership Platform, inda yake da burin samar da sabuwar Gwamnati mai jagorancin ta matasa, mai cike da hadin kai da kuma tsare-tsaren ayyuka ga al’ummar.
A cewarsa, shugabancin Yanzu na kasar ya zama na wasu tsiraru kuma baya samarwa talakawa saukin rayuwa, kana siyasar kasar ta koma ta gaba-gaba da rarrabuwar kai.
Rahoton DWAfrica ya Ambato Elwangu na shan alwashin yaki da matsalar rashin aikin yi ga matasa, gyaran fannin kiwon lafiya da ilimi, da kuma inganta zaman lafiya a yankuna.