Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai zama a San Gabriel Valley, Abiola Femi Quadri, hukuncin ɗaurin shekara 11 da wata 3 a gidan yari, bisa damfarar tallafin COVID-19 da ake bai wa marasa aikin yi da masu lalura ta musamman da ya kai dala miliyan 1.3 daga jihohin California da Nevada.
Quadri, mai shekaru 43, an kama shi ne bayan ya shigar da fiye da buƙatun 100 na bogi ta hanyar amfani da sunayen mutane daban-daban da ya saci bayanansu, kuma ya yi amfani da kuɗin wajen gina wurin shakatawa da kasuwanci a Nijeriya.
Alkalin kotun tarayya ta Amurka, George H. Wu, ne ya yanke hukuncin, tare da umartar Quadri da ya biya kuɗin diyyar dala $1,356,229 da tara na dala $35,000, bayan ya amsa laifinsa.
Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata takardar manema labarai daga ofishin mai gabatar da ƙara na gwamnatin tarayya a gundumar California ta tsakiya, Ciaran McEvoy, a ranar Alhamis, 10 ga Yuli, 2025.