Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar Majalisar Dattawa daga jihar Kogi da aka dakatar, ta shigar da ƙara ga Majalisar Dattawa tana neman su girmama hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta bayyana dakatarwar wata shida da aka yi mata a matsayin wuce gona da iri.
Kotun, a hukuncin da ta yanke a ranar 4 ga Yuli, ta umurci majalisar da ta duba yiwuwar dawo da sanatar kan kujerarta, tana mai cewa dakatarwar ta sabawa kundin tsarin mulki da kuma ‘yancin wakilcin jama’arta.
A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 11 ga Yuli, 2025, da lauyoyinta na M.J. Numa & Partners LLP suka tura wa majalisar, Sanata Natasha ta bukaci a cika duka sharuddan hukuncin da Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke.
Ta kuma bayyana shirinta na komawa bakin aiki ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, tana mai cewa dakatarwar ta sabawa tsarin mulkin ƙasa.
