Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu yau Lahadi a birnin London da misalin ƙarfe 4:30 na yamma bayan doguwar jinya.
Shugaba Tinubu ya sha mika ta’aziyyarsa ga uwargidan marigayin, Hajiya Aisha Buhari, tare da umartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da ya tafi Birtaniya domin dawo da gawar shugaban zuwa gida Najeriya.
Buhari ya shugabanci Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na mulkin farar hula daga 2015 zuwa 2023, kuma ya rike kujerar shugaban ƙasa a lokacin mulkin soja daga shekarar 1984 zuwa 1985.
A wani mataki na girmamawa, Shugaba Tinubu ya umarci a sauke tutar Najeriya zuwa rabin sanda a fadin kasar, a matsayin alamar alhini da karramawa ga rayuwar marigayin shugaban ƙasa.