Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da shirye-shiryen jana’izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 a wani asibiti a birnin London.
A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Litinin, Gwamna Radda ya bayyana cewa bayan tuntuba tsakanin iyalan marigayin da wasu na kusa da shi a London, an cimma matsaya cewa za a kawo gawar Buhari zuwa Katsina da misalin karfe 12 na rana ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025.
Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a garin Daura, mahaifar marigayin.
Gwamna Radda ya bayyana alhini da ta’aziyya ga iyalan Buhari da daukacin ‘yan Najeriya bisa wannan babban rashi na jarumin kasa.