Kamfanin Meta da ke da mallakin shafin sada zumunta na facebook ya bayyana gyara a shafin, inda ya sanar da cire shafuka Miliyan 10 na bogi da kuma na damfara 500,000 a farkon rabin shekarar 2025.
Meta ya sanar da yin hakan a matsayin wani mataki domin dakile masu shafukan sojan gona, kwaikwayo da kuma mu’amalar bogi don inganta asalin masu aiki da kuma yada su.
Kamfanin ya kuma kara da cewa, matakin ya shafi masu dauko ayyukan wasu ba tare da izini ba ko kuma sauya-sauye a cikinsa. Hukuncin ba zai tsaya ga rasa damar samun kudade ba a shafin, har da raguwar masu kallo ko mu’amala da aikin mutum a Facebook.