Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar Olabode Abimbola Ibikunle, malami a sashen kula da harkokin Jama’a na Jami’ar Prince Abubakar Audu, Anyigba.
Rahotanni sun bayyana cewa Ibikunle ya kai wata daliba, Miss Glory Ojochegbe Samuel (24GE1034), ɗaliba a sashen da yake koyarwa, zuwa wani otal a Anyigba, inda aka ce ya rasu yana tare da ita.
Bayan haka, dalibar ta sanar da ma’aikacin otal ɗin wanda suka garzaya da mamacin zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, William Aya, ya ce an tsare dalibar a hedikwatar ‘yan sanda da ke Lokoja domin gudanar da bincike na musamman a sashen binciken manyan laifuka na rundunar.
A nata bangaren, jami’ar Prince Abubakar Audu ta bayyana bakin cikinta kan lamarin, tana mai cewa wannan al’amari ne mai matuƙar tayar da hankali da kuma buƙatar cikakken bincike.