DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna Radda bai ji mummunan rauni ba bayan hatsarin mota – Gwamnatin Katsina

-

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tsira daga wani karamin hadarin mota da ya afku a yammacin Lahadin nan a hanyar Daura zuwa Katsina, yayin da yake gudanar da ayyukan gwamnati na yau da kullum.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar ta tabbatar da cewa gwamnan bai samu wani mummunan rauni ba, kuma yana cikin nutsuwa da koshin lafiya.

Google search engine

”Gwamna Radda yana cikin koshin lafiya kuma ba a samu wani rauni mai tsanani ba. Har ila yau, yana cikin karsashi da kwarin gwiwa,” in ji sanarwar.

Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa kariyarsa, tare da nuna godiya ga al’ummar jihar Katsina da sauran masu fatan alheri bisa addu’o’i da damuwa da suka nuna bayan samun labarin hadarin.

Sanarwar ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa cewa gwamnan na katsina ya ji mummunan rauni, inda sanarwar gwamnatin Katsina ta ce a halin da ake ciki, gwamnan ya ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da tangarda ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

ADC ta sake tabbatar da Sufiyanu a matsayin shugaban Kebbi, wani tsagi ya nuna turjiya

Ƙungiyar Shugabannin Jam’iyyar ADC a Jihohin Najeriya ta sake tabbatar da Engr. Bala Sufiyanu a matsayin sahihin shugaban jam’iyyar na jihar Kebbi, daidai lokacin da...

Farashin shinkafa ya karye a kasuwannin Legas

Farashin shinkafa ya sauka sosai a kasuwanni da dama na birnin Legas, sakamakon yawaitar shigowar shinkafa ta kan iyakoki. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya...

Mafi Shahara