Jam’iyyar ADC mai hamayya a Nijeriya ta soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ta bayyana a matsayin gazawa wajen cika alkawarin da ya dauka a yakin neman zaben 2023 na samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba cikin shekaru hudu.
A cikin wani sako da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar a shafin X, ya ce jam’iyyar ta zargi gwamnatin Tinubu da nuna halin ko in kula da yanayin wutar lantarki duk da karin kudin wuta da kuma wahalhalun rayuwa da jama’a ke fuskanta.
Jam’iyyar ta jaddada cewa fiye da shekaru biyu da fara mulkin Shugaba Tinubu, babu wani sauyi na a zo a gani da aka samu a bangaren samar da wuta, babu wata hanya ta tsare-tsare da aka fitar don inganta fannin, kuma babu wani ci gaba da za a iya aunawa wajen fadada hanyoyin samun lantarki.
A maimakon haka, ADC ta ce ‘yan Nijeriya sun shaida karin farashin wuta da yawan katsewar layin rarraba wuta na kasa a yankunan karkara.