Majalisar dattawa a Najeriya ta karɓi Sanatoci hudu daga jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC, lamarin da ya ƙara karfafa rinjayen APC a zauren majalisar.
Sanatocin da suka sauya sheka su ne: Sanata Ekong Samson daga Akwa Ibom South, da Sanata Etim Bassey Akwa Ibom North East, sai Sanata Francis Fadahunsi Osun East, da Sanata Olubiyi Fadeyi Osun Central.
Gidan talabijin na Channel ya tattaro cewa, bayan sauya shekar, APC yanzu tana da kujeru 72 a Majalisar Dattawa ta 10, daga 50 da ta fara da su a watan Yunin shekarar 2023.