Hukumar kwalon kafar kasar Italiya ta dakatar da mai tsaron ragar Nigeria Maduka Okoye na tsawon wattani biyu bisa zargin shiga harkar Caca da gangan
Dan wasan kwallon kafar mai taka Leda a kungiyar Udines ta gasar Seria A, ya tsallake rijiya da baya, bayan an kusa dakatar da shi na tsawon shekaru hudu kan laifin da ya fara.
Badakalar ta fara ne daga 11 ga watan Mayun shekarar 2024 a yayin wani wasa a gasar Serie A tsakanin kungiyar Udinese da kuma Lazio, inda Okoye ya karbi katin gargadi kan laifin bata a mintuna 64 da take wasan.