Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya ajiye kujerarsa a matsayin shugaban hukumar gudanarwar kamfanin Dangote Cement Plc, daga ranar 25 ga Yuli, 2025.
Wata sanarwa da kakakin kamfanin, Anthony Chiejina, ya fitar, ta bayyana cewa Dangote zai mayar da hankali sosai kan matatar mai, masana’antar sinadarai, takin zamani da kuma hulda da gwamnati, domin kara hanzarta ci gaban kasuwancin kamfaninsa cikin shekaru biyar masu zuwa.
Biyo bayan hakan, kamfanin ya sanar da Emmanuel Ikazoboh a matsayin sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar kamfanin.
Ikazoboh na daya daga cikin manyan daraktoci masu zaman kansu a hukumar.
Hakazalika, Mariya Aliko Dangote ta samu shiga cikin Hukumar Gudanarwar kamfanin, yayin da Farfesa Dorothy Ufot ta yi murabus.
Dangote Cement dai kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito na daya daga cikin manyan kamfanonin masana’antu a nahiyar Afirka, kuma yana taka muhimmiyar rawa a ci gaban tattalin arzikin Najeriya.