Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi, musamman na jam’iyyar APC, da su tabbatar da cewa makudan kuɗaɗen da aka raba musu ta hannun FAAC sun haifar da gamsassun ayyukan ci gaba, musamman a matakin ƙananan hukumomi.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC, inda ya jaddada cewa duk da rabar da Naira tiriliyan 11.195 ga jihohi da ƙananan hukumomi daga watan Yuni 2024 zuwa Yuni 2025, har yanzu mutane da dama na ƙara korafi kan rashin ayyukan ci gaba a matakin ƙasa.
Gidan talabijin na Channels ya ce binciken FAAC ya nuna cewa cikin Naira tiriliyan 27 da aka raba tsakanin Janairu zuwa Yuni 2025, gwamnatin tarayya ta samu Naira tiriliyan 6.034, jihohi sun samu Naira tiriliyan 6.492, yayin da ƙananan hukumomi suka karɓi Naira tiriliyan 4.704.
Har wa yau, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta tara Naira tiriliyan 14.27 a matsayin haraji cikin watanni shida na farkon shekarar 2025, karin 43% idan aka kwatanta da kudin haraji da aka tara a rabin farkon shekarar 2024.



