Duk da karin farashin wutar lantarki, al’ummar jihohi da dama a Najeriya na ci gaba da fama da karancin wuta da kuma rashin tabbas a samun ta, musamman a Kano, Borno, Kaduna, Lagos, Ogun, Binuwai da Filato.
Rahotannin da jaridar Daily Trust ta tattaro sun nuna cewa masu masana’antu da ‘yan kasuwa kanana na fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon karin farashin Band A, inda ake bukatar a ba su wuta har na sa’o’i 20 a rana, amma ba ta samuwa.
A Kano, masana’antun Sharada da Dakata na korafi kan cewa suna kashe miliyoyi Naira a wata, amma har yanzu sai sun dogara da janareto saboda rashin wadatacciyar wuta.
Masani a fannin sarrafa sharar robobi, Yusuf Bello Yakasai, ya ce yana biyan har Naira miliyan 4 a wata amma har yanzu bai samun ingantacciyar wuta.
A cewar hukumar NERC, kashi 53.2 cikin 100 na masu amfani da wuta a Najeriya ba su da mita, don haka ana ci gaba da karbar kudaden da aka kimanta ba bisa adalci ba.



