Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Najeriya na asarar kuɗi tsakanin Naira tiriliyan 13.3 zuwa Naira tiriliyan 17.9 a kowace shekara, saboda cutar hanta da tasirinta na kai tsaye da wanda ba na kai tsaye ba.
Rahoton jaridar Punch ta Ambato ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana hakan a taron manema labarai na bikin ranar ciwon hanta ta Duniya.
A cewarsa, Najeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashen uku mafi yawan masu ɗauke da ciwon hanta a duniya, inda mutane fiye da miliyan 20 ke dauke da cutar, ciki har da miliyan 18.2 da Hepatitis B, da miliyan 2.5 da Hepatitis C.
Ya kara da cewa a kowace shekara, cutar na kashe mutum 4,252 a Najeriya ta hanyar haddasa cancer hanta.