Hukumar NiMet ta bayyana cewa daga Litinin zuwa Laraba, za a samu guguwa da ruwan sama mai karfi a sassa da dama na Najeriya tare da yiwuwar ambaliya, musamman a Arewacin ƙasar.
A safiyar Litinin, za a samu ruwan sama mai karfi a Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe da Katsina, yayin da sauran jihohin Arewa za su fuskanci rana da dan hadari. Da yamma kuma, ana hasashen ya nuna za’a samu ruwan sama a Kebbi, Adamawa da Taraba.
A Talata da Laraba, hukumar ta yi hasashen ruwan sama da guguwa za su yawaita a jihohin Arewa da Kudu, ciki har da Kano, Katsina, Sokoto, Adamawa da Akwa Ibom, yayin da NiMet ke gargadin ambaliya a wasu sassan kudancin kasar.
Hukumar ta bukaci al’umma da su dauki matakan kariya da kuma gujewa wuraren da ruwa ke taruwa kamar yadda jaridar Daily Trsut ta tattaro.