Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai karɓi ‘yan wasan Super Falcons a fadar Aso Villa, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin Afirka ta Mata ta 2024 WAPCON.
Super Falcons sun lashe kofin karo na 10 bayan da suka doke ƙasar Morocco mai masaukin baki, a wasan ƙarshe da aka buga a Rabat.
Tuni Gwamnonin Nijeriya; Uba Sani na Kaduna, da AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, da Hope Uzodimma na jihar Imo, tare da ministocin tarayya, sun tarbi tawagar a filin jirgin saman Abuja domin nuna farin ciki da yabo ga nasararsu.
Haka kuma, ‘yan wasan Falcons hudu -Rasheedat Ajibade, Esther Okoronkwo, Michelle Alozie da Chiamaka Nnadozie, sun shiga cikin Best XI na gasar, inda CAF ta bayyana su a matsayin fitattun ‘yan wasa. Ajibade ce aka zaɓa a matsayin Mafi Kyawun ‘Yar Wasa a gasar.