Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa
A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar a birnin tarayya Abuja, shugaban na NNPCL Bayo Ojulari ya bayyana cewa ba za a cefanar da matatar ba sakamakon bukatar da ke akwai wajen gyarawa tare da bunkasa ta, hade da ta Warri da Kaduna domin amfanin Najeriya da al’ummarta, kamar yadda Punch ta wallafa.
Ojulari, ya ce sayar da matatar mai ta Fatakwal babu abun da zai haifarwa Nijeriya sai koma baya ga tattalin arzikin kasar.