Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya rushe majalisar zartarwar jiharsa gaba ɗaya, inda ya sallami dukkan kwamishinoni da kuma Shugaban Ma’aikata na fadar gwamnati.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kakakin gwamnan, Tersoo Kula, wanda ya bayyana cewa gwamnan ya sanar da wannan matakin ne a ƙarshen zaman majalisar zartarwa na 12 da aka gudanar a shekarar 2025.
Gwamna Alia ya umurci dukkan kwamishinoni da su mika ragamar mulki ga sakatarorin dindindin na ma’aikatunsu nan da nan ba tare da jinkiri ba.