DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An ceto matashi da ran sa bayan shafe sa’o’i 10 acikin baraguzan gini a Abuja

-

Wani matashi dan shekaru 27 daga Jamhuriyar Nijar, Aliyu Salisu, an ceto shi da ransa bayan shafe kusan sa’o’i 10 a cikin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya rushe a unguwar Lifecamp da ke Abuja.

Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh, ta fitar ranar Lahadi.

Google search engine

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 6:15 na yamma a ranar Asabar, inda aka samu kiran gaggawa. DPO na yankin Lifecamp ya gaggauta daukar mataki, ya tare wajen da lamarin ya faru tare da hadin gwiwar hukumomin ceto.

A cewar Adeh, da misalin karfe 4:00 na asuba ranar Lahadi, an ceto Aliyu Salisu da ransa daga cikin baraguzan ginin sannan aka garzaya da shi zuwa Asibitin Cedar Crest da ke Gudu domin kulawa da lafiyarsa.

Kwamishinan ’yan sanda na FCT, Ajao Adewale, ya yaba da jajircewa da hadin gwiwar jami’an ceto da mazauna yankin wajen ceto rayuwar matashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara