DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kananan ‘yan sanda masu karatun NCE/Dilpoma/Degree sun roki a karbi takardunsu a kara musu girma

-

Wasu jami’an ‘ƴan sanda masu ƙananan mukamai sun bukaci a jinkirta sabon tsarin ɗaukar aiki da rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ke shirin aiwatarwa, inda suka ce ya kamata a fara ba wa jami’an da ke aiki yanzu masu takardu dama ta haɓaka matsayin su bisa cancanta kafin a buɗe ƙofar sabbin daukar aiki.

A cikin wata wasika da suka aike wa  da DCL Hausa a kungiyance, jami’an sun bayyana damuwarsu kan yadda rundunar ke shirin ɗaukar sabbin ma’aikata da ke da takardu irin su NCE, Diploma da Degree, alhali kuwa akwai ɗimbin jami’an da ke aiki yanzu waɗanda suka mallaki waɗannan takardu amma ba su samu karin girma ba.

“Mun bar makaranta domin yi wa ƙasa hidima, muna fatan za a yaba mana ta hanyar kara mana girma ko sauya mana matsayi bisa cancanta. Amma yanzu ana shirin ɗaukar sabbi daga waje, alhali mu muna nan muna aiki da gogewa,” in ji wasikar.

Jami’an sun ce rashin wanzar da wannan dama na iya karya kwarin guiwar ma’aikata da kuma rage nagartar aiki a cikin rundunar, musamman idan aka ci gaba da nuna halin ko in kula ga waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu tun da farko.

Sun bukaci DCL Hausa da ta:
• Bayyana damuwar su ga jama’a da hukumomi,
• Wayar da kai kan muhimmancin bai wa ma’aikatan da ke aiki dama ta ci gaba,
• Taimakawa wajen ƙarfafa adalci da ɗaga kwarin guiwar jami’an da ke aiki a halin yanzu.

DCL Hausa na ɗaya daga cikin kafafen da ke sa ido kan batutuwan da suka shafi adalci da walwalar ma’aikata, kuma za ta ci gaba da bibiyar wannan batu domin tabbatar da an ji murya daga cikin rundunar.

Idan kai ma kana da labari ko ƙorafi da ya shafi adalci a ma’aikata ko tsakanin al’umma, aiko mana da saƙon ka ta hanyar DCL Hausa Facebook ko email info@dclhausa.com

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 bisa zarginsu da satar jarrabawa

Jami'ar tarayya da ke jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 daga karatu bisa samunsu da laifin satar jarabawa. Rahotanni sun...

Mafi Shahara