Liverpool ta fara shirya wa kare kambinta a gasar Premier League ranar Juma’a, 15 ga Agusta da Bournemouth a Anfield.
Kungiyar ta sabunta tawagarta da sabbin ‘yan wasa ciki har da Florian Wirtz Yuro miliyan 116.5, Hugo Ekitike, Jeremie Frimpong, Milos Kerkez da Mamardashvili, a karkashin kocin Arne Slot.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka bar kulob din sun hada da Trent Alexander-Arnold (Real Madrid), Luis Díaz (Bayern Munich), da Darwin Núñez wanda ke nazarin barin kulob din.
Slot zai ci gaba da amfani da tsarin 4-2-3-1 da ya kawo nasara bara, inda sabbin ‘yan wasan za su taka muhimmiyar rawa. Kulob din na fatan kare kambinsa bisa karfin da sabbin sauye-sauyen suka samar.