Tuna baya: a rana irin ta yau a shekarar 1996, Nijeriya ta lashe zinariya a gasar Olympics wadda aka gudanar a birnin Atlanta
A ranar 3 ga Agusta, 1996, ƙasar Najeriya ta kafa tarihi, bayan da ƴan wasan ƙwallon ƙafarta suka doke Argentina da ci 3-2, suka lashe zinariyar Olympics a gasar Atlanta.
Wannan ya zo ne bayan sun doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe ranar 31 ga Yuli.
Ƙungiyar ta U-23 wacce aka fi sani da Dream Team, ta ‘yan kasa da shekaru 23 ta shigar da Najeriya cikin kundin tarihi a matsayi na farko a Afirka da ta taɓa lashe zinariyar Olympics a kwallon ƙafa