DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shin bidiyoyin Dan Bello na nuna cewa akwai gibi tsakanin abin da gwamnatin Kano ke cewa ta yi da yadda talaka ke rayuwa?

-

Shin bidiyoyin Dan Bello na nuna cewa akwai gibi tsakanin abin da gwamnatin Kano ke cewa ta yi da yadda talaka ke rayuwa? Ko kuwa irin wannan bidiyo ne shiryayye don rage darajar gwamnati a idon jama’a? Wane bangare na alkawuran da aka ce an cika, har yanzu ke da shakku a zuciyar mutane?

Bidiyoyin da Dan Bello ya fitar a baya-bayan nan musamman kan yanayin makarantun gwamnati da sauran matsalolin da suka shafi jin dadin rayuwar al’umma a jihar Kano sun jefa tambaya mai nauyi kan ingancin kaso 85% na alkawuran da Gwamnan Kano ya ce ya cika.

Google search engine

Yayin da gwamnati ke tsayawa kan cewa ta samu nasarori masu yawan gaske cikin shekaru biyu da suka wuce, wasu na kallon sabbin bidiyoyon Dan Bello a matsayin wani bincike mai zurfi da ka iya murɗa agogon yabon nasara zuwa sa’o’in nazari da tambaya.

Mun bude wannan fili ne don masu bibiyar DCL Hausa su bayyana ra’ayinsu cikin girmamawa da gaskiya.

Shin bidiyon Dan Bello ya tabbatar da gazawa ko dai wata dama ce da gwamnati za ta iya amfani da ita don sake daidaita komai?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara