Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa sabon alkawarin da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi, ya sake yi na yin wa’adi daya kacal idan aka zabeshi shugaban kasa, wani nau’i ne na makirci da ruɗu.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023 yana da tarihi na saba alkawari da rashin gaskiya a siyasa.
Da yake mayar da martani kan kalaman Obi a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Lahadi, Onanuga ya ce wannan alkawari bai da tushe, yana kuma nuna cewa Obi bai cancanci shugabantar kasa mai sarkakiya kamar Najeriya ba.
Alkawarin wa’adin shekaru da Peter Obi ya yi wani salon makirci ne – Fadar Shugaban Nijeriya
-


