DCL Hausa Radio
Kaitsaye

APC ta fara samun baraka a wasu jihohin Nijeriya in ji wani binciken jaridar Punch

-

Duk da cewa jam’iyyar APC na rike da iko a matakin tarayya da kuma jihohi 23, tana fuskantar mummunan rikici na cikin gida da ke kara ta’azzara.

Rikice-rikicen bangaranci, zargin ƙaƙaba shugabanci, da rashin warware matsalolin jagoranci sun fara kawo barazana ga hadin kan jam’iyyar yayin da ake shirin fuskantar babban zaben 2027.

A cewar jaridar Punch, yawancin reshen jam’iyyar da ke cikin rudani sun haɗa da Lagos, Rivers, Delta, Bayelsa, Benue da Akwa Ibom.

Google search engine

Wannan ya tilasta shugabannin jam’iyyar a matakin kasa shiga tsakani domin shawo kan rikicin da ke barazanar dagula tsarin mulki da tasirin siyasar jam’iyyar.

A baya-bayan nan, APC ta sha fama da rabuwar kai da rikicin shugabanci da ke barazana ga daidaituwarta, duk da karbar wasu fitattun ’yan adawa ciki har da wasu gwamnoni da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara