Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta farfado da kamfanin saka na United Nigeria Textiles (UNTL) da ke Kaduna, wanda ya daina aiki tun 2022.
Sanusi ya bayyana hakan ne yayin da Ministan ma’aikatar masana’antu, Sanata John Enoh, ya kai ziyarar aiki da tuntubar masu ruwa da tsaki domin farfado da bangaren masana’antar yadi da tufafi a Najeriya.
Sanusi ya ce kamfanin ya taba bai wa sama da mutane dubu 10,000 aiki, kuma rushewarsa ya haifar da tasiri mai muni musamman ga matasa da mata, lamarin da ke iya kara tsananta rashin tsaro a yankin.



