DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kwamishinanmu ba shi da alaka da mai safarar kwayoyi, Danwawu – Kwamitin Gwamnatin Kano

-

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin duba gudunmawar da Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi Dala, ya bayar wajen tsayawa wanda ake zargi da safarar ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu, a matsayin mai karbar beli. Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya miƙa rahoton a wata ganawa da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Kano. Kakakin Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya tabbatar da wannan ci-gaba cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Rahoton kwamitin ya nuna cewa kwamishinan ne da kansa ya nemi izini don karbar belin  wanda ake zargi a ranar 18 ga Yuli, 2025, tare da rantsewa a cikin wata takardar shaidar rantsuwa cewa shi jami’in gwamnati ne kuma ya fahimci sharuddan beli. Duk da haka, kwamitin ya gano cewa bai  yi taka-tsan-tsan kafin ɗaukar wannan mataki ba, kodayake yana da cikakken sani kan laifin safarar ƙwayoyi da kuma matsayin gwamnatin jiha na yaki da miyagun ƙwayoyi da laifukan da ke shafar matasa. Haka kuma, kwamitin bai sami wata shaida ta alaka ta baya tsakaninsa da wanda ake zargi ba, kuma babu wata hujjar da ta nuna an ba shi wani cin hanci kafin tsayawa Danwawu. Har ila yau, kwamitin ya tabbatar cewa ba kwamishinan ne ya biya kuɗin beli na Naira miliyan biyar ba.

Google search engine

Gwamna Yusuf ya yaba wa kwamitin bisa yadda suka gudanar da aikinsu cikin kwarewa da adalci, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta duba shawarwarin kwamitin cikin zurfi. Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci wani nau’i na rashin da’a ba, tare da sake tabbatar da kudirinsa na gaskiya, adalci da ɗawainiya a harkar mulki—musamman wajen yaki da safarar ƙwayoyi da sauran laifukan da ke barazana ga makomar matasan Kano ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sabon shugaban hukumar zaben ya yi alwashin dawo da ingantacce da sahihin zabe a Nijeriya

Sabon shugaban hukumar zaɓen Nijeriya, INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya sha alwashin dawo da sahihanci da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe na ƙasar, yana...

Ba ni ke tsoma baki a gwamnatin Kano ko raba kwangiloli ba – Rabi’u Musa Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya karyata zargin da ake yi masa na tsoma baki a harkokin mulkin...

Mafi Shahara