DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun sace mata 20 a wani sabon hari a jihar Zamfara

-

A kalla mata da ‘yan mata 20 ne ‘yan bindiga suka sace a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, yayin da suke neman itace a wajen gari a ranar Asabar.

Wani mazaunin yankin, Sufyanu Moriki, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, yana mai cewa har yanzu masu garkuwar ba su nemi kudin fansa ba.

Google search engine

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar ya ce hukumar su ba ta samu bayani kan lamarin ba tukuna.

Rahotanni sun bayyana cewa hadin gwiwar ‘yan ta’adda da mayaka ma su da’awar jihadi na kungiyar Lakurawa a yankin na kara dagula lamarin tsaro a Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ka fito ka bayyana wa ‘yan Nijeriya hakikanin dalilin da ya sa ka canza hafsoshin tsaro – Bukatar ADC ga shugaba Tinubu

Jam’iyyar ADC ta bukaci shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana gaskiya ga ’yan Nijeriya kan ainihin dalilan da suka sa aka yi gaggawar sauya shugabannin...

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya nada yayansa a matsayin Sarkin Duguri

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya naɗa yayansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sarkin sabon masarautar Duguri da aka ƙirƙira a jihar. Sakataren gwamnatin Jiha, Aminu...

Mafi Shahara