Hukumar zaben Nijeriya INEC ta gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji fara yakin neman zabe gabanin zabukan 2027, inda ta bayyana hakan a matsayin karya dokar zabe.
Gargadin na INEC ya zo ne a daidai lokacin da ake samun yawaitar tarukan siyasa a fadin kasar, da sanya allunan hotunan ‘yan takara a allunan talla.
Sakataren yada labaran shugaban hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce har yanzu hukumar ba ta fitar da jadawalin zaben 2027 ba.
Kazalika ba a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu ba, kuma babu wata jam’iyyar siyasa da ta fitar da sunayen ‘yan takara a babban zaben mai zuwa ba,yin hakan ya sabawa sashi na 94,(1) na dokar zabe ta 2022.



