Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su jajirce wajen gina jam’iyyun siyasa da suka fi karfin gwamnati bin doka da oda.
Obi ya bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen taron baje kolin litattafai guda biyu da shahararren dan jarida Ike Abonyi ya rubuta.
Obi, yayin da ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da jajircewa wajen gina sabuwar Nijeriya, ya shawarci ‘yan kasar musamman ‘yan jarida masu zurfin ilimin siyasar Nijeriya su kara rubutawa mutane abinda zasu karanta cikin fahimtar yanayin siyasar Nijeriya.



