DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Davido ya ce ya zuba dala milyan 3.7 fiye da Naira bilyan biyar a bikin aurensa da Chioma

-

Shahararren mawakin Afrobeats, David Adeleke (Davido), ya bayyana cewa ya kashe dala miliyan 3.7 kwatankwacin Naira biliyan biyar, da miliyan dari shida da sittin da bakwai, a shirye-shiryen bikin aure na fari da matarsa, Chioma, da za a yi a Miami wannan karshen mako.

Bikin zai kasance na uku ga ma’auratan, bayan na kotu a Maris 2023 da na gargajiya a Legas a Yuni 2024.

Google search engine

Taron zai sami halartar fitattun ’yan Najeriya, ciki har da Gwamnan Osun, Ademola Adeleke.

Davido da Chioma sun fara haduwa sama da shekara 10 da ta gabata, kuma sun fuskanci kalubale, ciki har da rasuwar dansu Ifeanyi a 2022, kafin su haifi tagwaye a 2023 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya tattaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnonin da suka sha suka ta yanzu sun koma jam’iyyar APC – Ministan Abuja Wike

Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ficewar wasu gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC ta tabbatar da goyon bayansa ga Shugaba...

Majalisar Dattawan Nijeriya za ta tantance sabon shugaban INEC ranar Alhamis

Majalisar Dattawan Nijeriya ta shirya tantance Farfesa Joash Amupitan, wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zaba domin zama sabon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, a...

Mafi Shahara