DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin litar man fetur na nan yadda yake ba mu kara ba kan Naira 850 – Matatar man Dangote

-

Matatar man Dangote ta bayyana cewa farashin litar man fetur a masana’antar yana nan daram a ₦850, tare da karyata jita-jitar cewa an kara farashi ko kuma an dakatar da aiki.

Jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Anthony Chiejina, ya ce masana’antar na aiki yadda aka saba ba tare da wata matsala ba, tana samar da sama da lita miliyan 40 na fetur a kullum, tare da isasshen dizal (Automotive Gas Oil).

Google search engine

Ya kara da cewa sayar da Residual Catalytic Oil (RCO) lokaci-lokaci bangare ne na harkokin kasuwanci na yau da kullum, ba wata alama ce ta tsaiko ko rufe aiki ba, duk da rade-radin da ake yadawa kamar yadda rahoton gidan talabijijn na Channels ya ruwaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon kwamishinan Ganduje ya soki gwamnatin Abba bisa zargin sayar da filin makarantar

Tsohon kwamishinan ilimi na a zamanin Ganduje, Muhammad Sanusi Sa'id Kiru, ya soki matakin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mayar da Makarantar Sakandare ta ‘Yan...

Hukumar zabe za ta hada kai da majalisar wakilan Nijeriya domin gudanar da sahihin zabe

Shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da Majalisar Dokoki domin tabbatar da gudanar da sahihin...

Mafi Shahara